20 Janairu 2022 - 10:10
​Ganawar Shugabannin Iran Da Rasha A Birnin Moscow

A ziyarar aiki da ya fara a birnin Moscow, shugaba Ibrahim Ra’isi na Iran, ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Yayin ganawar shugaban Ra’isin, ya bayyana cewa babu wani cikas wajen bunkasa alaka tsakanin jamhuriyar musulinci da kuma tarayyar Rasha.

‘’ba mu da iyaka a bunkasa alaka da ci gaba tsakanin Moscow da Tehran’’ inji shugaban kasar ta Iran.

Ya kuma yabawa Rasha game da yaki da ta’addancin da take a kasar Siriya.

Da ya tabo batun yarjejeniyar nukiliyar Iran kuwa, shugaba Ra’isi ya bayyana cewa kasarsa na fadi rashin ganin an dage mata haramtatun takunkuman da Amurka ta kakaba mata.

A nasa bangare kuwa shugaba Putin, ya nuna jin dadi matuka game da ziyarar ta takwaransa na Iran.

Ya kuma aike da sako na fatan alhairi ga jagoran juyin jya halin musulinci na Iran, Ayatollah Khamenei.

342/